in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe wasu mutane biyu dake samar da abinci ga kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Nijeriya
2017-09-30 13:06:14 cri
Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe wasu mutane biyu masu samar da abinci da kayayyaki ga mayakan Boko Haram, yayin wani kwantan bauna da suka yi musu a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Kakakin Rundunar Timothy Antigha ya ce an kama 'yan ta'addan ne yayin da suke tafiya kan dawakai 14 a kauyen Malamti dake yankin Guzamala na jihar a ranar Alhamis.

Timothy Antigha ya shaidawa manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar cewa, sojoji biyu sun samu rauni yayin musayar wuta da ya biyo bayan kwantar baunan.

Ya kara da cewa, dakarun sun kwato alburusai da kayayyakin abinci da na ciye-ciye da dabbobi daga hannun 'yan ta'addan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China