Nazarce-nazarcen da mujallar lafiya ta Amurka ta wallafa, sun bayyana hanyoyi 2 mabanbanta da za su hana kwayar cutar dake haddasa zazzabin yaduwa cikin sauki a tsakanin sauro.
A cewar cibiyar binciken kiwon lafiya ta Johns Hopkins Bloomberg, binciken ya bude wata kofa ta samar da hanyoyin takaita samun zazzabin malaria ta hanyar daukar dabarun kare kariya.
Amfanin wannan shi ne, zai rage bukatar ci gaba da amfani da matakan kariya kamar amfani da maganin kashe kwari ko gidan sauro. (Fa'iza Mustapha)