Babban minista Yaw Osafo Maafo, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar cewa, an bukaci hukumomin tsaro su tabbatar da aiwatar da kunshin dokar.
Da yake jawabi ga wani taro kan harkokin kiwon kifi da yankunan ruwa a birnin Accra, Yaw Maafo ya ce illar da kamun kifi ta haramtacciyar hanya ke yi wa sana'ar kifi a Ghana, ya zarce wanda hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba ke yi koguna da dazuka da gonaki.
Ya ce an dade ana jadadda bukatar mutane su yi biyayya ga dokokin da suka shafi kiwo da kamun kifi bisa radin kansu, sai dai abun takaici shi ne, yadda galibin masu sana'ar suka gaza amsa kiran, al'amarin da ya ba haramtattun hanyoyin kamun kifi da mummunan tasirinsa ga kiwon lafiya da tattalin arziki wajen zama. (Fa'iza Mustapha)