in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta karfafa dangantaka da Angola
2017-09-28 09:34:19 cri

Jakada na musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, Chen Yuan, ya nanata aniyar gwamnatin Sin wajen karfafa kyakkyawar dangantaka da kasar Angola, kasar wadda ta rantsar da sabon shugabanta a ranar Talata.

Chen, ya gabatar da sakon taya murna da fatan alheri na shugaba Xi ga sabon shugaban kasar Angolan Joao Lourenco, a lokacin da jakadan na Sin ya halarci bikin rantsar da Lourenco, kana ya samu ganawa da sabon shugaban kasar a ranar Talata.

Jakadan na musamman ya ce, kasar Sin tana fatar yin musayar kwarewa da kasar ta Angola, kana tana fatar karfafa kyakkyawar mu'amala da zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

A nasa bangaren, Lourenco ya bayyana cewa, bisa irin taimakon da kasar Sin ke baiwa Angola, a halin yanzu, kasar ta samu gagarumin ci gaba a bangarori da dama, musamman fannin ababan more rayuwa.

Ya ce, kasar Angola ta dora muhimmanci game da kyakkyawar huldar dake tsakaninta da kasar Sin, kana kasar tana maraba da kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar ta Angola domin samun moriyar juna da ci gaban bangarorin biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China