Yayin wani taron tattaunawa mai taken "mukalu kan hanyoyin sarrafa shara" a wani bangare na babban taron Afrika kan fannin injiniya, masanan sun ce gazawar kasashen Afrika na sarrafa shara yadda ya kamata ta hanyar sake juya shi, ka iya zama babban kalubale ga kawar da shara a nahiyar.
Kasar Rwanda ce ta karbi bakuncin taron da aka fara daga ranar 25 zuwa 29 ga wata nan, mai taken "ingantacciyar hanyar sarrafa shara a Afrika" wanda ke kara mai da hankali kan inganta kwarewa a fannin injiniya a Afrika domin samar da kayayyakin more rayuwa. (Fa'iza Mustapha)