in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan matan Afirka su taka rawa a fannonin kimiyya da injiniya
2017-09-27 09:48:18 cri
Masana sun shawarci kasashen Afrika su karfafa wa mata gwiwar shiga a dama da su a fannonin kimiyya da injiniya da sauran fannonin da ake samun rashin daidaiton jinsi.

Masanan sun bayyana haka ne yayin wata tattaunawa kan shigar mata fannonin kimiyya da injiniya a Afrika, a wani bangare na babban taron nahiyar Afrika kan fannin injiniya da aka kaddamar a ranar Litinin a birnin Kigali na Rwanda.

Kasar dake yankin tsakiyar Afrika ta karbi bakuncin taron dake gudana tun daga 25 zuwa 29 ga watan nan mai taken "ingantacciyar hanyar sarrafa shara" wanda ke mai da hankali kan inganta kwarewa a fannin injiniya a Afrika, domin samar da kayayyakin more rayuwa.

A cewar shugabar kwamitin gudanarwa ta kungiyar injiniyoyi ta duniya Valerie Agberagba, akwai bukatar su mai da ilimin kimiyya da injiniya yadda za su ja hankalin mata.

Ta bayyana cewa, kashi 30 cikin dari na mata ne kadai ke taka rawa a fannin, kuma rashin daidaiton ya fi yawa a nahiyar Afrika.

Masanan sun kuma alakanta rashin samun damar yin karatu tsakanin mata da 'yan mata a matsayin daya daga cikin dalilan da suka sa ake samun karancin mata a wadannan fannoni.

A nata bangaren, babbar daraktar kula da ilimin kimiyya da fasaha ta ma'aikatar ilimi ta kasar Rwanda Christine Gasingiwa, cewa ta yi, karfafa wa dalibai mata karantar fannonin kimiyya da injiniya shi ne jigo na samun karin adadin kwararru da za su magance kalubalen da ci gaban ababen more rayuwa ke fuskanta a fadin Afirka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China