in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci yankunan yammaci da tsakiyar Afrika su yi amfani da dimbin albarkatun da suke da su
2017-09-26 10:09:00 cri

Jami'an dake halartar taro karo 9, na yammaci da tsakiyar nahiyar Afrika kan hakar ma'adinai a birnin Accran kasar Ghana, sun tabbatar da cewa, yankunan biyu sun mallaki wasu albarkatu fiye da ko ina a duniya.

Da take bude taron, mataimakiyar ministan filaye da albarkatu na Ghana Barbara Oteng-Gyasi, ta ce wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa yankunan suka zamo cibiyar zuba jari kan harkokin hakar ma'adinai a nahiyar Afrika.

A don haka, mataimakiyar ministar ta yi kira da a lalubo hanyoyin da kasashen Afrika wadanda suka mallaki ma'adinai, za su yi amfani da su wajen samar da ci gaban zaman takewa da tattalin arziki a nahiyar.

Taron na yini biyu da kamfanin hakar ma'adinai na Magenta Global ya shirya, ya samu mahalarta da masu baje koli daga kasashen Ghana da Benin da Burkina Faso da Senegal da sauran wasu kasashen Afrika da na Turai da Amurka.

A daidai lokacin da kamfanin Magenta Global ke farfadowa daga kalubale mafi tsanani da ya fuskanta a baya-bayan nan, babbar jami'ar zartarwa ta kamfanin Maggie Tan, ta ce yankunan yammaci da tsakiyar Afrika sun dawo fagen jan hankalin jama'a. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China