in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shawarci kasashen Afirka da su sanya hannu kan yarjejeniyar kan iyaka
2017-09-26 09:41:04 cri

Babban darektan cibiyar nazarin manufofin da suka shafi makamashi ta Afirka (ACEP) Benjamin Boakye ya yi kira ga kasashen Afirka da su tsara, su kuma adana muhimman bayanai, kana su sanya hannu kan yarjeniyoyin da suka shafi kan iyaka, a wani mataki na warware duk wata takadda mai nasaba kan iyaka tsakanin kasashen nahiyar, wadanda galibi an gaje su ne daga Turawan mulkin mallaka.

Wata sanarwa da babban darektan cibiyar ya fitar, ta bayyana cewa, fayyace kan iyakan ko wace kasa, zai taimaka wajen samar da tabbas tare da janyo masu sha'awar zuba jari.

Cibiyar ACEP ta ce, rikicin kan iyaka tsakanin kasashen Ghana da Cote d'Ivoire zai fargar da kasashen Afirka kan yadda za su fito da kan iyakokin su, kana su adana duk wani muhimman bayanai da suka shafi hakan.

A ranar Asabar din da ta gabata ce kotun kasa da kasa dake kula da dokokin da suka shafi iyakokin ruwa (ITLOS) ta yi watsi da korafin da kasar Cote d'Ivoire ta shigar a gabanta cewa, kasar Ghana ta shiga iyakarta yayin da take aikin hako mai a yankin da ake takaddama a kai. Inda kotun dake da matsuguni a birnin Hamburg na kasar Jamus ta gabatar da sabbin ka'idoji game da shata kan iyakan ruwa tsakanin kasashen biyu.

A cewar cibiyar ta ACEP, sakamakon abubuwa da aka gano kan iyakokin kasashen, akwai yiyuwar kara gano wasu abubuwan da ka iya harzuka kasashen, wanda daga bisani zai bukaci raya filaye da ayyuka na hadin gwiwa tsakanin sassan biyu.

A halin da ake ciki dai, an bukaci gwamnatin kasar Ghana da ta shata iyaka tsakaninta da kasar Togo mai makwabtaka, don kaucewa aukuwar irin wannan rikici a nan gaba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China