in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari ya ba da umarnin a kwashe 'yan Najeriya da suka makale a tsibirin Dominica
2017-09-26 08:56:35 cri

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayar da umarnin a gaggauta kwashe 'yan kasarsa da suka makale a tsibirin Dominica dake yankin gabashin Caribbean, sakamakon mahaukaciyar guguwar nan ta Maria da ta yi illa a tsibirin.

Mai magana da yawun fadar shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu wanda ya tabbatar da wannan umarni a jiya Litinin, ya ce nan ba da dadewa ba za a kwashe dalibai 'yan Najeriyar da ke wannan tsibiri zuwa kasar Brazil, inda ba sa bukatar takardar Viza kafin daga bisani a dawo da su zuwa gida Najeriya.

Rahotanni na cewa, yanzu haka ministan harkokin wajen Najeriyar ya tura wani babban jami'i daga ma'aikatar don ganin an baiwa daliban da suka makale takardun tafiye-tafiye na wucin gadi, ta yadda za a hanzarta kwashe su.

A kalla mutane 10 ne mahaukaciyar guguwar ta Maria ta halaka, inda ta karade yankin na Caribbean da ruwan sama da iska mai karfin gaske, yayin da ta ratsa ta gabar tekun gabashin yankin a ranar Alhamis din da ta gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China