Barzani ya shaidawa taron manema labarai cewa, babu gudu babu ja da baya game da shirinsu na kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan wannan batu, duk da kiraye-kiraye da matsin lambar da suke fuskanta daga gwamnatin Bagadaza, da kasashe makwabata da Amurka kan su dakatar da kada kuri'ar ta yadda za a koma kan teburin sulhu.
Barzani ya ce, tattaunawar da suke yi da gwamnatin Bagadazan ta rushe, har ma firaministan Iraki Haider al-Abadi ya mayar da martani cikin fushi, inda ya nanata cewa, ba ya goyon bayan shirin kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da kwarya kwaryar nemen 'yancin kai na yankin.
A don haka, Barzani ya ce yanzu kan bakin alkalami ya riga ya bushe. (Ibrahim Yaya)