in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsawaita wa'adin aiki ga sojojin kasar Turkiya da su gudanar da ayyukan soja a Iraki da Syria har na tsawon shekara daya
2017-09-24 13:22:03 cri
A jiya Asabar, majalisar dokokin kasar Turkiya ta zartas da wani kuduri, inda aka tsawaita wa'adin aiki ga sojojin kasar Turkiyyar da su ci gaba da gudanar da ayyukan soja a Iraki da Syria har na tsawon shekara guda.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Anadolu na kasar Turkiya ya bayar, an ce, jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar ce ta gabatar da kudurin, sa'an nan majalisar dokokin kasar Turkiyya ta jefa kuri'u tare da zartas da kudurin a gun taron musamman da aka gudanar a wannan rana.

Kafin hakan, majalisar dokokin kasar Turkiyya ta tsaida wa'adin aiki na sojojin kasar don su gudanar da ayyukan soja a kasashen Iraki da Syria daga ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar 2016 zuwa ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2017.

Manazarta sun yi tsammanin cewa, wannan ne matakan da kasar Turkiyya ta dauka don tinkarar batun jefa kuri'un jin ra'ayoyin jama'a da za a gudanar a yankin Kurdistan na kasar Iraki, manufarta shi ne taimakawa gwamnatin kasar wajen gudanar da ayyukan soja a kasashen waje.

A watan Yuni na bana, yankin Kurdistan na kasar Iraki ya sanar da aniyarsa na kada kuri'ar raba gardama kan samun 'yancin kansa a ranar 25 ga watan Satumba, yayin da gwamnatin tsakiya ta kasar Iraki da kasashen Turkiya da Iran da sauran kasashen dake makwabtaka da yankin sun ki amincewa da kudurin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China