in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika su sayi ingantattun magungunan kasashen Sin da Indiya
2017-09-23 13:33:18 cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bukaci kasashen Afrika dasu sayi ingantattun magunguna masu saukin kudi daga kasashen Sin da Indiya domin ceto lafiyar al'ummarsu.

Daraktar sashen kula da magunguna da kayayyakin kula da lafiya na hukumar WHO Suzanne Hill, ta bayyana cewa an tabbatar da wadannan magunguna da kasashen biyu ke samarwa suna da matukar inganci wajen yaki da cututtukan dake yaduwa a yankuna masu fama da zafi.

Hill ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, magungunan cuta mai karya garkuwar jiki wato "HIV/AIDS, da na malariya, da magungunan dake rigakafin kamuwa da kwayoyin cuta wadanda ake samar da su daga kasashen Sin da Indiya ana iya samunsu a cibiyoyin kiwon lafiya na kasashen Afrika, kuma an yi amanna cewa magungunan suna da matukar inganci kuma suna yin tasiri wajen inganta lafiyar jama'ar nahiyar ta Afrika".

Jami'ar ta bukaci gwamnatocin kasashen Afrika su fara hada magungunan a cikin gida kuma su tabbatar da sun samar da magunguna masu inganci wadanda zasu samar da ingantacciyar lafiya ga al'ummarsu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China