in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a sanadiyyar girgizar kasa a Mexico ya karu zuwa 273
2017-09-22 10:30:45 cri

Gwamnatin kasar Mexico ta ce, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 7.1 da ta auku a ranar Talata, ya karu zuwa 273.

Rabin mace-macen ya auku ne a birnin Mexico City, inda kusan gine-gine 40 suka rushe, yayin da sauran suka auku a kewaye da jihohi dake kusa da birnin.

Akwai yiwuwar adadin zai karu yayin da ake ci gaba da aikin ceto, inda ake zakulo gawarwaki daga cikin baraguzan gine-gine da suka rushe a sanadiyyar girgizar kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China