Shugaban Sudan Omar Al-Bashir, ya bukaci mazauna yankin Darfur da su mika makamansu ga gwamnati bisa radin kansu, kafin gwamnati ta fara karba da karfi.
Da yake jawabi ga wani taron jama'a a birnin Nyala, babban birni jihar Darfur ta Kudu, shugaba Al-Bashir ya ce, da gaske suke game da batun kwace makamai, kuma abu mafi dacewa ga duk wani da ya mallaki bindiga shi ne ya mika bindigar ga hukuma.
Ya kara da cewa, dole ne duk wani da ya boye makami ya mika shi ga gwamnati bisa radin kansa. (Fa'iza Msutapha)