in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika da su rungumi tsarin kirkiro sabbin irin shukawa don samar da abinci a nahiyar
2017-09-21 14:09:13 cri
Masana sun shawarci kasashen nahiyar Afrika dasu rungumi tsarin kirkiro sabbin irin shukawa da nufin bunkasa samar da abinci da tabbatar da cigaban aikin gona mai dorewa.

Kwararrun sun yi kiran ne a lokacin taron dandalin kungiyar tarayyar Afrika na shiyya game da aiwatar da yarjejeniyar samar da tsirrai da nufin bunkasa shirin samar da abinci da habaka aikin gona (ITPGRFA) a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

Kasar Rwanda ce ta karbi bakuncin taron daga ranar 19 zuwa 20 ga watan Satumba inda taron ya share fagen babban taron shugabanni na ITPGRFA wanda za'a gudanar a Kigali karo na 7, wanda zai gudana daga 30 ga watan Oktoba zuwan 3 ga watan Nuwambar wannan shekarar.

Taron na wuni biyu, ya janyo hankalin kwararru a fannin aikin gona daga nahiyar Afrika har ma da sauran sassa na duniya domin tattauna muhimmanci da irin gudunmowar da sabbin tsirrai zasu bayar wajen habaka aikin gona da samar da wadataccen abinci a fadin nahiyar, inda matsalar abinci ta kasance babban abin da ke ciwa nahiyar tuwo a kwarya a halin yanzu.

Janet Edeme, mai rikon mukamin daraktar sashen kula da tattalin arzikin yankunan karkara da habaka aikin gona na kungiyar tarayyar Afrika, ta bukaci gwamnatoci da cibiyoyi a Afrika da su samar da yanayi mai kyau ga sabbin tsirrai domin su ba da gudunmowa wajen yaki da talauci da kawar da matsalar yunwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China