in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka suna hadin gwiwa domin raya aikin jigilar kayayyaki kan teku a Afirka
2017-09-20 10:55:31 cri

A birnin Abidjan dake kasar Kwadibuwa, manyan jiragen ruwan kasar Sin sama da goma suna gudanar da aikin sake gina tashar ruwa dake birnin, wanda shi ma babban birnin tattalin arzikin kasar, daga sama, ana iya kallon wannan sabuwar babbar tashar ruwa da za a rika sauke manyan akwatunan zuba kayayyaki, wadda za ta kasance tashar ruwa irinta mafi girma a yammacin nahiyar Afirka.

Mataimakin babban manajan kamfanin gina tashar ruwa na kasar Sin reshensa a yammacin Afirka wanda ke gudanar da aikin sake gina tashar ruwa ta Abidjan Wang Guangsheng yana ganin cewa, sake gina tashar ruwan yana da babbar ma'ana, inda ya bayyana cewa, yanzu tashar ruwa ta Abidjan tana iya sauke manyan akwatunan zuba kayayyaki da yawansu ya kai dubu 650 a ko wace shekara, bayan da za a kammala aikin aka gina ta, yawan manyan akwatunan zuba kayayyakin da za ta iya saukewa zai karu zuwa kusan miliyan daya da dubu 900, lamarin da zai kara bunkasa tattalin arzikin kasar ta Kwadibuwa matuka.

Abu mafi jawo hankalin jama'a yayin da ake gudanar da aikin sake gina tashar ruwar Abidjan shi ne, kamfanin kasar Sin ya yi amfani da fasahar zamani wadda ta kai matsayin koli a duniya, misali, an kafa babban ginin tashar ruwan nan da manyan akwatunan da aka kera da karafa da siminti, wadanda kuma tsayinsu ya zarta mita 19, kana nauyinsu ya kai kusan tan 3200.

Wang Guangsheng ya yi alfahari sosai kan fasahar da kamfaninsa ke amfani da ita, inda ya ce, irin wadannan akwatunan karafa da siminti da za a zubar da su cikin ruwan teku sun ba da mamaki ga al'ummar kasar ta Kwadibuwa, har ma sun ba da mamaki ga masanan aikin gina tashar ruwa na kasashen Turai da Amurka baki daya, saboda su ma ba su taba ganin irinsu ba a baya.

An fara gudanar da aikin sake gina tashar ruwar Abidjan ne tun daga watan Satumban shekarar 2015, adadin kudin da za a kashe kan aikin ya kai dalar Amurka miliyan 933 da dubu 400, bankin shige da fice na kasar Sin ne ya samar da rancen kudin, kwararrun da abin ya shafa na kasar ta Kwadibuwa suna ganin cewa, bayan sake gine-gine, tashar ruwar Abidjan za ta kasance tashar ruwa mafi girma a yammancin Afirka, ita ma za ta taka muhimmiyar rawa wajen raya siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu a kasar.

Nahiyar Afirka tana kewaye ne da ruwan teku, idan ana son raya tattalin arziki a duk fadin nahiyar, wadda ke kumshe da kasashe masu tasowa mafiya yawa, kamata ya yi a kara mai da hankali kan aikin jigilar kayayyaki a kan teku, amma a halin da ake ciki yanzu, duk da cewa, akwai tasoshin ruwa da yawa a kasashen Afirka, amma yawancinsu ba su iya sauke akwatunan zuba kayayyaki da dama ba, dalilin da ya sa haka shi ne domin gine-ginensu sun tsufa, bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta yi, an ce, yawancin tasoshin ruwan kasashen Afirka suna iya sauke manyan akwatunan zuba kayayyakin da yawansu bai kai miliyan daya ba a ko wace shekara, amma a tashar ruwan Shanghai na kasar Sin, ko wace shekara, ana iya sauke manyan akwatunan zuba kayayyakin da yawansu ya kai miliyan 36, a saboda haka, an fara sake gina tashar ruwa a kasashen Afirka a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kamfanin kasar Sin kuwa ya fi samun karbuwa daga wajen su bisa ingancin aikinsa da farashi mai rahusa da kuma aiwatar da aikin cikin gajeren lokacin.

Kawo yanzu gaba daya adadin tasoshin ruwan da kamfanin gina tashar ruwa na kasar Sin ya gina a kasashen Afirka ya riga ya kai 11, misali a kasar Aljeriya, kamafanin yana gudanar da aikin gina tashar ruwa ta Hamdaniya dake da nisan kilomita 60 daga Algiers, babban birnin kasar, an ware dalar Amurka biliyan daya da miliyan 500 kan aikin, za a kafa wuraren sauke manyan akwatunan zuba kayayyaki 23, inda za a iya sauke manyan akwatunan zuba kayayyakin da yawansu zai kai miliyan 6 da dubu 300 a ko wace shekara.

To, idan ana son yin amfani da tasoshin ruwan yadda ya kamata, dole ne a hada su da sauran birane da layin dogo, domin jigilar kayayyakin cikin sauri, shi ya sa ba ma kawai kamfanin kasar Sin ya samar da taimako kan aikin gina tashar ruwa a kasashen Afirka bane, har ma ya taimake su wajen gina layin dogo, da haka za a iya jigilar da kayayyakin da aka sauke daga jirgin ruwa da jirgin kasa zuwa sauran wuraren dake nesa da bakin teku. Misali, a kasar Kenya, kamfanin kasar Sin ya gina tashar ruwa ta Mombasa, wadda ta fi girma a gabashin nahiyar a shekarar 2013, yanzu haka yana gudanar da aikin gina tashar ruwa ta Lamu a kasar, kana layin dogo dake hada Mombasa da Nairobi ya riga ya fara aiki, don haka ana gudanar da aikin jigilar kayayyaki a gabashin Afirka lami lafiya.

Ana saran, aikin jigilar kayayyaki ta kan teku na kasashen Afirka zai kara bunkasa karkashin kokarin da sassan biyu wato Sin da Afirka suka sanya cikin hadin gwiwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China