Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya yi gargadi game da safarar makamai da 'yan tawaye masu dauke da makamai a kan iyakar kasar ta Sudan da jamhuriyar Chadi.
Al- Bashir ya bayyana cewa, kan iyakar kasashen biyu ba waje ne na yin safarar makamai ba, sai dai waje ne na yin musaya domin amfanin kasashen. Ya bayyana hakan ne a lokacin wani rangadi wanda ya fara a yankin Darfur a ranar Talata, yankin dake fama da yakin basasa tun daga shekarar 2003.
Ya bayyana hadin gwiwar dakarun kasar Sudan da na Chadi a matsayin wani abin koyi na hadin gwiwa tsakanin kasashen dake makwabtaka da juna, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dandazon jama'a a El Geneina, babban birnin jihar yammacin Darfur.(Ahmad Fagam)