in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika za su yaki safarar bishiya ba bisa ka'ida ba
2017-09-20 09:59:59 cri

Kasashen Afrika sun sha alwashin yaki da masu safarar bishiyar ta haramtattun hanyoyi da sauran albarkatun da ake samarwa daga dazuka domin tabbatar da ganin albarkatun da ake samu a dazukan sun bayar da gudunmowa wajen ci gaban tattalin arziki na GDP na kasashen.

Babban jami'in kula da gandun daji na kasar Kenya Emilio Mugo, ya bayyana cewa, wakilai daga kasashen Kenya, Uganda, Mozambique, Madagascar, Tanzania da Zanzibar wadanda suka yi taro a Nairobi a ranar Talata, sun amince za su dauki tsauraran matakai kan wadanda suka kama da laifin yin safarar albarkatun dajin ta haramtattun hanyoyi.

Mugo ya bayyana a karshen taron na wuni biyu cewa, taron wani muhimmin mataki ne a yunkurin tabbatar da dakile yin safarar bishiya a kudancin Afrika ba bisa ka'ida ba, ta yadda za'a sauya akalar cinikayyar don amfanin dukkan al'ummomin kasashen.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China