Da yake tsokaci game da hakan, Mr. Wang ya yi fatan ganin MDD ta kara fadada rawar da take takawa a harkokin duniya, musamman a wannan lokaci da kalubale ke daduwa a sassa daban daban. Ya ce Sin za ta hada kai da MDD wajen ganin an inganta dangantakar kasa da kasa, da zuba karin jari domin samar da ci gaba, tare da daukar matakan wanzar da zaman lafiya, duka dai da nufin dakile matsaloli da duniya ke fuskanta.
Har wa yau, a yayin ganawar sa da Miroslav Lajcak shugaban zama na 72 na MDDr dake gudana a yanzu haka, ministan na harkokin wajen kasar Sin, ya jinjinawa kokarin majalissar bisa managartan manufofi da take aiwatarwa.(Saminu Alhassan)