in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da aikin sake gine gine bayan gangarowar laka a Saliyo
2017-09-19 10:27:29 cri

A ranar 14 ga watan Agustan bana ne bala'in gangarowar kasa ya auku a wani yanki na birnin Freetown, fadar mulkin kasar ta Saliyo, kuma kawo yanzu, kusan wata guda da aukuwar hakan, cikin kwanaki kusan talatin, an riga an fara gudanar da aikin sake gina sassan da bala'in ya fadawa.

Bayan aukuwar bala'in gangarowar laka a birnin Freetown na kasar Saliyo a watan Agustan da ya gabata, an fara gudanar da aikin sake gina wuraren yadda ya kamata. Kuma duk da cewa har yanzu mazauna birnin musamman wadanda bala'in ya addaba suna cikin bakin ciki matuka, kokarin da ake yi na samar da goyon baya da tabbaci ga bukatun su na rayuwar yau da kullum na da matukar ma'ana.

Alkaluman da aka fitar daga hukumar kididdiga ta kasar Saliyo sun nuna cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu yayin aukuwar bala'in zabtarewar lakar ya zarta dubu daya, kana mutane sama da dubu daya sun rasa muhallansu. A halin da ake ciki yanzu, gwamnatin kasar da hukumomin da abin ya shafa na kasar, na kokari matuka wajen gudanar da ayyukan sake gina birnin, musamman ma a yankunan da suka fi fama da wahalhalu. Yanzu haka an riga an kafa rumfunan tsugunar da mutanen da suka rasa muhallansu irin na wucin gadi masu yawa, kuma an samar musu wasu kayayyaki domin biyan bukatunsu. Misali gado da gidan sauro da dai sauransu. Kana ofishin hukumar tsaron kasar shi ma ya na samar da abinci sau 2 a kullum gare su, tare kuma da samar musu ruwan sha da magunguna.

Kakakin ofishin tsaron kasar ya bayyana cewa, kawo yanzu an riga an kafa rumfunan da yawansu ya kai kusan dari daya, kuma ana tsugunar da mutane biyar zuwa shida ko ashirin a cikin ko wace rumfar bisa girmanta.

Wani mutum da ya rasa muhalli ya gaya mana cewa, iyalansa guda takwas suka rasa rayukan su a yayin bala'in, ban da shi da ya tsira da rai daga bala'in, ya ce, har yanzu yana jin tsoro matuka. Ya ce a ranar da ibtila'in ya auku, ya ji karar wani abu, daga baya ya ga gangarowar kasa ta fado daga tudu cikin sauri, sai ya gudu nan take, babu lokacin gargadin saura, a saboda haka mutane da dama suka rasa rayukansu.

Bayan aukuwar masifar, wasu kungiyoyin jin kai na kasa da kasa sun samar da tallafin kudi da kayayyaki ga wadanda ke cikin mawuyacin hali. Misali, wata kungiyar jin kai ta kasa da kasa ta samar da kudin tsugunar da mutanen har tsawon watanni uku, kana ko wanen iyalin da masifar ta addaba yana iya samun tallafin kayayyakin da darajarsu ta kai wajen dalar Amurka dari daya a watan Satumba, a watan Oktoba da na Nuwamba kuwa, za su iya samun tallafin kayayyakin da darajarsu za ta kai dalar Amurka kusan ashirin da biyar.

Ban da haka kuma, ana mai da hankali sosai kan aikin samar da abinci ga masu bukata. Tun daga watan Satumbar da muke ciki kuma, gwamnatin kasar na samar da abinci kai tsaye ga ko wanen iyali. Ya zuwa watan Oktoba da na Nuwamba kuwa, za ta samar da tallafin kudi gare su domin su sayi abinci da kansu. Kazalika, wani kamfanin sadarwa ya samar da wayar salula ga masu bukata.

Mataimakin shugaban kasar ta Saliyi Victor Fo, yana kula da aikin ba da tallafi ga mutanen da suke shan wahalhalun bala'in, inda ya bayyana cewa, kawo yanzu an riga an samu tallafin da yawansa ya kai dalar Amurka sama da miliyan daya, kuma gwamnatin kasar za ta yi amfani da kudaden domin gudanar da aikin sake gina wurin.

Domin hana sake aukuwar bala'in a nan gaba, gwamnatin kasar ta Saliyo tana shirin kwashe mutane mazauna wurin dake daura da duwatsu dake birnin Freetown zuwa wani wuri na daban. A halin da ake ciki yanzu, kamfanonin gina gidaje guda uku suna gina gidaje domin tsugunar da su a karkarar birnin. An kimanta cewa, bisa mataki na farko, za a gina gidaje har guda 50.

Abun bakin ciki shi ne bayan aukuwar bala'in, yara sama da dari daya sun rasa iyayensu, sun kasance marayu, kuma a yanzu haka an riga an tsugunar da su a cikin wata cibiyar ba da agaji dake birnin Freetown. Gwamnatin kasar da wasu mutane, tare da wasu hukumomin da abin ya shafa, za su samar da tallafi ga wadannan yara marayu. Abu mai faranta ran mutane shi ne wasu daga cikin su, sun riga sun koma makaranta domin ci gaba da yin karatu tun daga ranar 11 ga watan nan. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China