in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da sabon shirin samar da ruwan sha mai tsabta a garin Somali
2017-09-19 10:18:34 cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF da gwamnatin yankin Puntland ta kasar Somali, sun kaddamar da wani shirin hadin gwiwa da nufin samar da ruwan fanfo mai tsabta ga dubban jama'a na garin Bosasso.

Karkashin wani shirin hadin gwiwa na gwamnati da hukumomi masu zaman kansu da UNICEF da hukumar samar da ruwa ta yankin Puntland, da sashen samar da makamashi da albarkatun kasa, da kamfanin GUMCO, za su gudanar da aikin gyaran tankokin ruwan sha da kuma shimfida bututun ruwa sama da mita dubu 10, domin gyaran hanyoyin samar da ruwan sha da suka lalace a garin Bosasso. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China