in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci bikin bude ofishin jakadancin Sin da ke Panama
2017-09-18 13:36:27 cri

Jiya Lahadi 17 ga watan nan, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da shugaban kasar Panama Juan Carlos Varela, suka halarci bikin bude ofishin jakadancin Sin da ke Panama, a birnin Panama, hedkwatar mulkin kasar.

A cikin jawabin da ya gabatar, Wang Yi ya bayyana cewa, bude ofishin jakadancin kasar Sin da ke Panama, wani muhimmin lokaci ne a tarihin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Kuma da hakan Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta kafa hukumar diplomasiyya a Panama a hukumance. Ofishin zai kokarta wajen aiwatar da manufar gwamnatin kasar Sin ta sada zumunta da kasar Panama, kana zai hada kai tare da sassa daban daban na Panama, don bude wani sabon shafi ga hadin gwiwar kasashen biyu, da nufin cimma moriyar juna da samun bunkasuwa tare.

Bugu da kari, Wang Yi ya kara da cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Panama tana da makoma mai haske. Kuma wata hanya ce ta hadin gwiwa dake da kyakkyawar makoma, wadda za ta yi matukar amfani ga kasashen biyu.

Ya ce kasar Sin na da aniyar kara kwazo tare da bangaren Panama, wajen inganta amincewa da juna a siyasance, da karfafa hadin kansu wajen cimma moriyar juna, da kara fahimtar juna tsakanin jama'arsu, ta yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata a nan gaba.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China