in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi 17 ga Satumba a matsayin ranar hawan keke ta duniya
2017-09-18 11:08:17 cri

Kamfanin hayar keken Mobile na kasar Sin da hukumar kiyaye muhalli ta MDD wato UNEP, da hukumar kula da muhallan dan adam ta MDD wato UN-Habitat, da sauran hukumomin kasa da kasa cikin hadin gwiwa, suka zabi ranar 17 ga watan Satumbar ko wace shekara a matsayin ranar hawan keke ta duniya, domin sa kaimi ga al'ummomin kasashen duniya da su rika tafiye tafiya ba tare da gurbata muhalli ba.

Bana shekara ce ta cika shekaru 200 da aka fara amfani da keken hawa, ita ce kuma shekara ce da aka samu babban ci gaba a fannin hayar keke a fadin kasar Sin. A cikin kwanaki 500 da suka gabata, kekunan da ake haya daga kamfanoni sun kasance kayayyakin zirga-zirga mafiya muhimmanci na uku a biranen kasar Sin, wato a bayan motocin bas da kuma jiragen kasa dake karkashin kasa, ko shakka babu kekunan da ake hayar su daga kamfanoni, sun kawo babban tasiri ga muhallan dan adam.

Jagoran kamfanin hayar keken Mobike na kasar Sin Wang Xiaofeng ya bayyana cewa, kawo yanzu kamfaninsa ya riga ya samar da kekunan Mobike fiye da miliyan 7 a fadin duniya, domin masu tafiye tafiye su rika amfani da su, kana masu yin amfani da su sun riga sun zarta miliyan 150. A ko wace rana, adadin mutanen da suke hawa keken Mobike ya kai sama da miliyan 25, Wang Xiaofeng yana mai cewa, "A cikin wadannan kwanaki 500, gaba daya tsawon hanyar da masu hawan keken Mobike suka bi, ta kai kilo mita miliyan 5600, ko shakka ba bu, idan da sun hau mota ne a maimakon keke, za a fitar da gurbatacciyar iska har tan miliyan 1 da dubu 360, adadin da ya kai adadin gurbatacciyar iskar da motocin da yawansu ya kai dubu 350 za su fitar a duk tsawon shekara."

A saboda haka kamfanonin hayar keken Mobike na kasar Sin, da hukumar kiyaye muhalli ta MDD, da hukumar kula da muhallan dan adam ta MDD, da asusun kiyaye albarkatan hallitun duniya, da cibiyar nazari kan albarkatan duniya, da sauran hukumomin kasa da kasa, sun sa hannu kan wata takardar ba da shawara, inda suka zabi ranar 17 ga watan Satumba, a matsayin ranar hawan keke ta duniya, inda za a gudanar da ayyuka a jere a ranar a ko wace shekara, domin sa kaimi ga daukacin al'ummomin kasashen duniya, da su yi tafiye tafiya ba tare da gurbata muhalli ba.

Wakilan da suka halarci bikin kaddamar da aikin suna ganin cewa, kokarin da kasar Sin take wajen hayar keke ga jama'a domin kiyaye muhalli, ya kawo babban tasiri ga sauran kasashen duniya. Babban wakilin cibiyar nazari kan albarkatun duniya dake kasar Sin Li lailai ya bayyana cewa, kekunan da ake amfani da su ta hanyar yin haya daga wajen kamfanonin, za su kara taka rawa wajen ci gaban birane a cikin dogon lokaci, dalilin da ya sa hakan shi ne, kasancewar hawan keke ba zai gurbata muhalli ba.

Wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya dake kasar Sin Bernhard Schwartlander yana kaunar hawan keke, shi ma yana mai da hankali matuka kan kamfanonin hayar keken kasar Sin, ya ce, yanzu cikin sauki ana iya hayar keke daga wajen kamfanonin hayar keke da kudi kadan, hakan ya sa masu tafiye tafiye ke zabar hanyar hawan keke a cikin zaman rayuwarsu na yau da kullum. Ya kara da cewa, kasar Sin tana samun sabon ci gaba wajen kirkire-kirkire, wanda zai kara kyautata ingancin rayuwar al'ummar kasar, saboda hawan keke baya ga sassauta cunkuson sufuri, zai kuma samar da dama ga al'ummar kasa ta kara motsa jikinsu.

Darektan hukumar kula da muhallan dan adam ta MDD kan aikin kasar Sin Zhang Zhenshan ya bayyana cewa, kafa ranar hawan keke ta duniya, ya dace da bukatun ci gaban kasashen duniya; ciki hadda ajandar tabbatar da dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 da MDD ta tsara, da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, wadanda suka bukace al'ummomin kasa da kasa da su yi tafiye tafiye ba tare da gurbata muhalli ba, ta yadda za a samar da muhallin zaman rayuwa, da aiki mai inganci ga dan adam. Kana yana ganin cewa, yanzu haka an kafa ranar hawan keke ta duniya, a sa'i daya kuma, ya kamata a tattaunawa, domin kyautata matakan da ake dauka a wannan fanni inda ya ce, "Misali na ga mutanen da suke hawan keke a kasashen ketare su kan sa hula domin kare kansu, amma a kasar Sin, kusan kalilan ne suke amfani da hular, don haka kamata ya yi a dauki matakai na wajibi domin kyautata hawa kekuna. Kuma a wasu birane na kasar Sin, ba a kebe hanyoyi ko wuraren tafiyar kekuna da suka dace ba tukuna. A saboda haka, ya dace sassa daban daban da hakan ya shafa su kara azama tare, domin warware wadannan matsaloli yadda ya kamata."

Babban teken ranar hawan keke ta duniya ta farko ta bana ita ce "hawan keke zai canja birane".(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China