in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamas ta sanar da cewa za ta wargaza kwamitin kula da harkokin zirin Gaza
2017-09-18 09:10:59 cri

A jiya Lahadi ne kungiyar Hamas ta Palasdinu, ta sanar da cewa, za ta wargaza kwamitin kula da harkokin zirin Gaza, kuma ta amince da shirya babban zabe a Palesdinu, kuma tuni kungiyar Fatah da sauran jam'iyyun siyasa na Palestinu suka yi maraba da wannan kuduri na Hamas.

A cikin sanarwar, Hamas ta amince da gwamnatin sulhun da Palesdinu ta kafa game da harkokin zirin Gaza, tare kuma da aiwatar da yarjejeniyar sulhun da ta daddale da Fatah a birnin Alkahira na kasar Masar a shekarar 2011. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China