in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an 'yan sanda 3 da aka sace a yankin arewa maso yammacin Nijeriya sun kubuta
2017-09-17 13:47:14 cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kubutar wasu 'yan sanda uku da aka sace, inda ta ce suna cikin koshin lafiya.

An sace jami'an 3 ne a ranar 4 ga watan nan a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar, a lokacin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi wa wani karamin ofishin 'yan sanda tsinke a kauyen Tsafe na jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Shaba Alkali, ya ce daya daga cikin jami'an ya samu rauni sakamakon harbin da mutanen suka yi.

A cewarsa, rundunar da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro na aiki domin tabbatar da kama 'yan bindigar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China