in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bikin baje kolin jiragen sama masu saukar ungulu na kasa da kasa karo na 4 a Tianjin na Sin
2017-09-15 12:22:27 cri

Ana gudanar da bikin baje kolin jiragen sama masu saukar ungulu na kasa da kasa karo na hudu a yankin raya tattalin arzikin filin saukar jiragen sama na birnin Tianjin na kasar Sin, tsakanin ranekun 14 zuwa 17 ga wannan wata, inda kamfanonin kera jiragen sama masu saukar ungulu da dama daga sassa daban-daban na duniya suka halarci bajen tare da jiragen samansu.

Bikin baje kolin jiragen sama masu saukar ungulu da ake gudanarwa a birnin Tianjin, shi ne bikin baje koli na kasa da kasa daya kacal da kasar Sin ta samu damar karbar bakuncin shiryawa, kana shi ne bikin baje koli daya tak da aka yi wasa da jiragen sama a sararin samaniya a fadin duniya, kuma an shirya wannan baje kolin a kasar Sin ne ganin yadda kasuwar jiragen sama masu saukar ungulu a kasar ta ke bunkasa cikin sauri.

Zhang Xuetian wanda ke aiki a cibiyar ba da ceton jinyar gaggawa ta birnin Beijing ya halarci wannan baje kolin, saboda aikinsa na kula da harkokin dake shafar jirgin sama mai saukar ungulu yayin da ake gudanar da aikin ba da ceton jinya na gaggawa, Zhang Xuetian yana ganin cewa, makomar aikin ba da ceton jinya ta hanyar yin amfani da jirgin sama mai saukar ungulu tana da haske, shi ya sa ana bukatar kara sayen jirgin sama mai saukar ungulu a fannin aikin jinya, inda ya ce, "A halin da ake ciki yanzu, aikin ba da ceton jinya ta hanyar yin amfani da jirgin sama mai saukar ungulu yana kara samun karbuwa a wajen al'umma, don haka ya kamata a kara kera irin wadannan jirage domin biya bukatunsu, misali, a baya an sha fuskantar matsalar karancin motar ba da ceton jinya, nan gaba za mu kara sayen jiragen sama masu saukar ungulu domin ba da ceton jinya ga masu bukata."

Ban da ceton jinya, ana amfani da jirgin sama mai saukar ungulu wajen jigilar man fetur da binciken layin lantarki da tantance ma'adinai da kashe gobara da sauransu.

Wasu alkaluman bincike na nuna cewa, ya zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2017 da muke ciki, gaba daya adadin jiragen sama masu saukar ungulu da ake amfani da su a fannin aikin dake shafar fareran hula a babban yankin kasar Sin ya kai kusan 900. Kana kwamitin shirya wannan bikin baje kolin ya ruwaito kamfanin Airbus na cewa, yanzu a ko wace shekara a kalla kasar Sin tana sayen jirgi mai saukar ungulu dari daya daga kamfanin, adadin da ya zarta adadin jirgin sama mai saukar ungulu da kasar Amurka ta saya a ko wace shekara, lamarin da ya ba ta damar kasancewa a sahun gaba a kasuwar kamfanin a fadin duniya.

Ana iya cewa, karfin kasuwar jirgin sama mai sauka ungulu ta kasar Sin ta jawo hankalin kamfanonin kera jirgin sama na kasa da kasa, inda kamfanonin sama da 400 daga kasashe da shiyyoyi 22 a fadin duniya suka halarci bikin baje kolin, kana suka shiga ayyuka kusan 30, misali taron tattaunawa kan sabbin fasahohin kera jirgin sama da bikin daddale yarjejeniya da taron cudanyar kasuwanci da sauransu, kazalika, an shirya taron cudanya kai tsaye tsakanin kamafanoni har sau 200.

Kawo yanzu kasar Sin ta daddale wasu yarjejeniyoyin sayen jirgin sama mai saukar ungulu da wasu shahararrun manyan kamfanonin kera jirgin sama a fadin duniya kamar su Airbus da Bell da Leonardo domin sayen jrigin sama mai saukar ungulu fiye da 500, wadannan kamfanonin za su mika wa kasar Sin jiragen da za su kera a cikin shekaru goma masu zuwa. Kamfanin Airbus shi ke kan gaba a fannin, inda zai sayarwa kasar Sin jiragen da yawansu ya kai 50 a cikin shekara daya.

Glen Giammalva, 'dan kasar Amurka ne, kana matukin jirgin sama mai saukar ungulu na fararen hula, yanzu yana aikin ba da shawara kan aikin dake shafar jirgin sama, yana kuma horas da matukin jirgin sama na kamfanin kasar Sin, yana ganin cewa, duk da cewa, kasuwar jirgin saman kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri, amma ma'aikatan kasar dake yin aikin suna fuskantar kalubale, inda ya ce, "Ina ganin cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan aikin horas da ma'aikatan dake aiki a wannan sana'a, misali matukan jirgin sama da masu gyara jirgin sama da masu tafiyar da harkokin kamfanonin jirgin sama mai saukar ungulu da sauransu."

Babban manajan kamfanin Rockwell Collins na Amurka reshen kasar Sin He Weichang ya gabatar da shawarar cewa, idan kasar Sin tana son dakile wadannan kalubale, ya kamata ta hada gwiwa da kamfanonin kasashen Turai da kuma Amurka, inda ya bayyana cewa, "Misali a fannin fasaha, idan kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kamfanonin ketare, to, nan da nan za ta daga matsayinta, kamfaninmu shi ya yana iya amfana, saboda kamfanin kasar Sin ya fi fahimtar kasuwar cikin gida a kasar Sin, ana iya cewa, sassan biyu suna amfana tare."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China