in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta dakatar da samar da kudi ga majalisar Turai
2017-09-14 16:11:55 cri
Peter Tolstoy, mataimakin shugaban DUMA wato majalisar wakilai ta kasar Rasha, ya furta a yau Alhamis cewa, kasar Rasha ta dakatar da samar da kudi ga majalisar nahiyar Turai, wanda ake bukatar dukkan mambobin majalisar su biya.

Jaridar Izvestie ta kasar Rasha ta ruwaito Peter Tolstoy na cewa, kasar Rasha ta dauki wannan mataki ne saboda mai da ta saniyar ware, da majalisar ta yi, ganin yadda majalisar ta hana kasar damar jefa kuri'a a babban taron majalissu karkashinta.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China