in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNMISS ta fara kaddamar da sintirin dare don tabbatar zaman lafiya a Sudan ta kudu
2017-09-14 10:59:50 cri

Tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Suda ta kudu ko UNMISS a takaice, ta fara wani aikin sintiri da dare a wuraren da jama'a suka dawo, a wani mataki na kara samar da tsaro da tabbaci ga 'yan kasar Sudan ta kudu da suka dawo gida.

Shugaban tawagar ta UNMISS a Sudan ta kudu David Shearer ya bayyana a jiya Laraba cewa, mahukuntan Sudan ta kudu na duba shirin da tawagar ta bullo da shi.

Jami'in na MDD ya ziyarci yankunan dake makwabtaka da Lokololo dake wajen Wau, inda wasu magidanta suka dawo gidajensu har ma sun fara shuka abin da za a sanya a bakin salati.

Ya ce, tawagarsa a nata bangaren za ta taimaka da tsaro, a hannu guda kuma hukumomin agaji za su samar da karin hidimomi a wajen sansanonin tsaron da aka tanadarwa jama'a, ta yadda za a kara samar musu da abubuwan more rayuwa don fara rayuwa a gidajensu.

Shearer wanda har ila shi ne wakilin musamman na babban sakataren MDD, ya ce, yadda mutanen da aka raba da muhallansu suka dawo gidajensu a yankin na Wau, zai kasance abin koyi ga sauran sassan kasar.

Bayanai na nuna cewa, a cikin watanni da suka gabata yawan wadanda ke zaune a sansanonin tsaron fararen hula na tawagar ya ragu daga 38,000 zuwa 32,500. Kuma galibin mutanen sun dawo gida ne don su noma gonakansu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China