in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD na fatan saukaka harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama'a a shiyyar kafin karshen 2017
2017-09-14 10:01:43 cri

Kungiyar raya kasashen gabashin Afirka (IGAD) tana fatan ganin an gudanar da zirga-zirgar jama'a, kayayyaki da sauran hidimomi tsakanin kasashe 7 dake cikin wannan kungiya ba tare da wani shamaki ba kafin karshen wannan shekara ta 2017 da muke ciki.

Shugaban ofishin kungiyar dake kasar Sudan ta kudu Abdelrahin Ahmed Khalil shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi yayin taron tuntubar juna game da tanade-tanaden kungiyar a kan zirga-zirgar jama'a a shiyyar. Ya ce, yanzu haka kungiyar ta fara tattaunawa da daukacin kasashe mambobinta, don tabbatar da cewa, an amince da wannan yarjejeniya kafin karshen wannan shekara.

Khalil ya ce, taron yana fatan tattara muhimman bayanai da shawarwari game da fa'ida ko akasin haka kan zirga-zirgar jama'a ba tare da shinge ba a tsakanin kasashen kungiyar, wanda daga karshe za a kai ga cimma matsaya tsakanin kasashe 9 mambobin kungiyar kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da za ta amince da zirga-zirgar jama'a a shiyyar ba tare da wani shamaki ba.

Manufar wannan yarjejeniya da ake fatan cimmawa ita ce, a halatta zirga-zirga da al'ummomin kasashen kungiyar ke yi a shiyyar ta IGAD da kuma kara samar da damammaki a hukumance.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China