in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya sanar da wasu tsare-tsaren sake fasalin majalisar
2017-09-14 09:21:25 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya sanar da wasu tsare-tsare biyu da suka danganci zaman lafiya da daidaiton jinsi.

Antonio Guteress wanda ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Laraba gabanin babban taron mahawara na zauren majalisar, ya sanar da kafa wani sabon kwamitin ba da shawarwari kan batun shiga tsakani.

Ya ce, kwamitin zai kunshi fitattun mutane 18 daga kasashen duniya, wadanda ke da gogewa da basira da ilimi mai zurfi game da muhimmin aikin.

Mambobin kwamitin sun hada da Michelle Bachelet, shugabar Chile, da Graca Machel, uwargidan marigayi Nelson Mandela, da Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Nijeriya, da kuma Justin Welby, babban limamin mabiya addinin Kirista na Canterbury.

Har ila yau, sakatare janar din ya sanar da wata manufar majalisar ta daidaito jinsi, wadda ke da nufin cimma daidaito a tsakanin manyan jami'an majalisar zuwa shekarar 2021, sannan ya mamaye baki dayan majalisar zuwa shekarar 2028.

Tun daga watan Janairu, mata ne suka samu fiye da rabin mukaman da ya nada, inda ake da mata 17 da maza 15, wadanda suka hada da sabbin mukamai da kuma wadanda aka sabunta.

Ya ce, za a nada mata mukamai masu yawa domin a yanzu adadin maza ya rinjaye na mata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China