in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kiran da a hada kai domin yaki da masu aikata laifuffuka ta yanar gizo
2017-09-13 10:08:07 cri

Jiya Talata ne masu gabatar da kara da dama wadanda suke halartar taron shekara shekara na kunigyar masu gabatar da kara ta kasa da kasa karo na 22 da babban taron wakilan kungiyar, suka tattauna kan laifuffukan da ake aikatawa ta yanar gizo, inda suka bayyana cewa, idan ana son warware wannan matsalar da ta addabi daukacin kasashen duniya a halin yanzu, kamata ya yi su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Shugaban hukumar gurfanar da mutane a gaban kotu ta lardin Hubei dake kasar Sin wanda ke halartar taron Wang Jin ya bayyana cewa, yanzu haka ana fuskantar laifuffukan da ake aikatawa ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohi ta yanar gizo, don haka ba zai yiyu wata kasa guda ta dakile matsalar ita kadai ba, ya zama wajibi kasashen duniya su kara yin cudanya, ta yadda za a dakile matsalar tare cikin nasara.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China