in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru: Ana shawarar kasashen Afirka da su inganta hanyoyinsu na tattara bayanan yanayi don samun ci gaba mai dorewa a nahiyar
2017-09-13 09:45:09 cri
An yi kira ga kasashen nahiyar Afirka da su zamanantar da hanyoyinsu na tattara muhimman bayanai game da yanayi, da ruwan kogi a wani mataki na samun ci gaba mai dorewa a sassan nahiyar.

Taron dandalin ministocin nahiyar na farko game da yanayi(AMCOMET) shi ne ya ba da wannan shawara, yana mai cewa, ta haka ne kadai nahiyar za ta warware duk wasu matsaloli game da matsalar canjin yanayi da batun samar da ruwan sha mai tsafta, matsalolin da suka kasance gagarabadau ga duniya baki daya.

Taron wanda kungiyar tarayyar Afirka(AU) tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar Habasha suka shirya, ya kuma cimma matsaya game da bukatar inganta sashen kula da harkokin yanayi na nahiyar.

A jawabinsa yayin taron kwamishinan kula da tattalin arzikin yankunan karkaka na hukumar kungiyar tarayyar Afirka Josefa Sacko, ya jaddada muhimmancin dake akwai na bullo da nagartattun manufofi da dabaru game da kara inganta hanyoyin samun muhimman bayanai kan hasashen yanayi da ma yanayin kansa.

Taron da ya gudana tsakanin ranakun 12 zuwa 15 ga watan Satumba da muke ciki, ya samu halartar wakilai daga kasashen Afirka,malaman jami'o'i,shugabannin sassa masu zaman kansu da kungiyoyin kasa da kasa. Inda su ma suka yi kira da a samar da kwararru wadanda za su taimaka wajen magance aukuwar bala'u da matsalar canjin yanayi a nahiyar a dogon lokaci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China