in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da baje kolin hotunan sakamakon da Sin ta samu wajen kiyaye hakkin dan adam a Geneva
2017-09-12 13:07:19 cri

An kaddamar da baje kolin hotuna game da sakamakon da kasar Sin ta samu wajen tabbatar da al'umma mai wadata da kiyaye hakkin dan adam jiya Litini a fadar "palace of nations" dake Geneva. Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin da hadin gwiwar zaunanniyar tawagar wakilan kasar Sin dake MDD ne suka shirya baje kolin. Karon farko ke nan da kasar Sin ta shirya irin wannan baje koli kan hakkin dan adam yayin taron hukumar kiyaye hakkin dan adam ta MDD.

A jiya ne aka kaddamar da taron hukumar kiyaye hakkin dan adam ta MDD karo na 36 a fadar "palace of nations" dake birnin Geneva na kasar Switzerland, yayin taron, a karon farko, kasar Sin ta shirya baje kolin hotuna game da sakamakon da ta samu wajen tabbatar da al'umma mai wadata da kiyaye hakkin dan adam, inda aka nuna wa 'yan kallo hotuna sama da 70 da kuma bidiyon da aka dauka guda 15 wadanda ke bayyana nasarorin da gwamnatin kasar Sin ta samu a fannonin yaki da talauci da samar da ilmi da aikin yi da kiwon lafiya da demokuradiya da tafiyar da harkokin kasa bisa dokoki da kula da harkokin addini da kananan kabilu da harkokin mata da yara da tsofaffi, da samar da tallafi ga kasashen ketare da suke da bukata da sauransu, baje kolin dake nunawa al'ummomin kasashen duniya babban ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kiyaye hakkin dan adam, tare kuma da nunawa al'ummomin kasashen duniya kokarin da take na ciyar da sha'anin kiyaye hakkin dan adam gaba a fadin duniya.

Yayin bikin kaddamar da baje kolin, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, wato tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje a kasar ta Sin, musamman ma a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar ta samu gagarumar nasara wajen kiyaye hakkin dan adam, haka kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga ci gaban sha'anin kiyaye hakkin dan adam na duniya, inda ya ce, "Ana gudanar da wannan baje kolin a daidai lokacin da ya dace, wato za a kaddamar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 nan ba dadewa ba, haka kuma za a bude taron hukumar kiyaye hakkin dan adam ta MDD karo na 36, a saboda haka ana iya cewa, baje kolin na da babbar ma'ana. ba nunawa al'ummomin kasashen duniya babban sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin kiyaye hakkin dan adam kadai zai yi ba, har ma da kara zurfafa fahimtar sauran kasashe kan kokarin da muke yi a fannin."

Mai sa ido kan aikin kiyaye hakkin dan adam na hukumar kula da harkokin kiyaye hakkin dan adam ta ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin Huang Junxie ya bayyana baje kolin a matsayin mai ma'ana ta musamman, ya na mai cewa, "Aikin kiyaye hakkin dan adam yana da muhimmanci matuka, yanzu kasar Sin tana kokarin cimma burin tabbatar da al'umma mai wadata, ko shakka babu hakan zai kyautata zaman rayuwar al'umma, al'amarin da zai kara kyautata aikin kiyaye hakkin dan adam a kasar."

A nasa bangaren, zaunannen wakilin kasar Pakistan dake MDD Farukh Amil cewa ya yi, hotunan da aka nuna sun bayyanawa al'ummomin kasashen duniya babban sakamakon da kasar Sin ta samu wajen kiyaye hakkin dan adam, ya na mai cewa, bai kamata wasu kasashe su zargi yanayin da hakkin dan adam ke ciki a kasar Sin ba, saboda zargin ba shi da tushe bare makama. Inda ya ce, "Aikin da gwamnatin kasar Sin ke yi shi ne, samar da ruwan sha mai tsabta da damar samun ilmi da guraben aikin yi ga al'ummar kasar domin kiyaye hakkinsu, tare kuma da samar musu da muhallin zaman rayuwa mai inganci."

Babban jami'in hukumar kula da 'yan ci rani ta duniya William Lacy Swing shi ma ya jinjinawa ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kiyaye hakkin dan adam, inda ya ce, "A kowacce shekara, na kan kai ziyara kasar Sin, a don haka, na ganewa idona ci gaban da ta samu, musamman ma wajen yaki da talauci, ko shakka babu kasar Sin za ta ci gaba da bunkasa a nan gaba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China