in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin Sin ya yi bayani kan kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2375
2017-09-12 12:19:00 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2375 a jiya Litinin, kan gwajin nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ta yi. Dangane da wannan batun, mista Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa wasu tambayoyi da manema labarai suka yi masa a yau Talata.

A cewar kakakin, kasar Koriya ta Arewa ta yi biris da ra'ayin da gamayyar kasa da kasa suka nuna na kin amincewa da matakanta, inda ta sake gudanar da gwajin nukiliya, abun da ya keta kudurin kwamitin sulhu na MDD. Saboda haka, kasar Sin ta amince da kwamitin sulhun ya dauki makatan da suka wajaba.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan burinta na kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya, da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da neman daidaita matsalar ta hanyar shawarwari.

Ya ce, ya kamata Koriya ta Arewa a nata bangaren, ta kiyaye kudurin kwamitin sulhun tare da dakatar da aikin kirkiro makaman nukiliya. Yayin da a nasu bangare, Amurka da Koriya ta Kudu, kamata ya yi, su magance daukar matakan da za su tsananta yanayin da ake ciki a zirin Koriya.

Mista Geng Shuang, ya kara da cewa, dole ne a daidaita batun ta hanyar lumana, kuma kasar Sin ba za ta yarda a tada wutar rikci a zirin Koriya ba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China