in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Nijeriya ta kai farmaki ta sama kan babbar maboyar mayakan Boko Haram
2017-09-12 09:50:53 cri
Rundunar sojin Nijeriya, ta kai hari ta sama, kan wani gini da ya kasance maboyar mayakan Boko Haram, a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojin saman kasar Tokunbo Adesanya, ya bayyana a jiya cewa, sun yi ammana mayakan kungiyar da ba a san adadinsu ba sun mutu yayin harin da aka kai ranar Alhamis da ta gabata.

A cewarsa, wuta ta tashi a ginin da aka kai wa harin a yankin arewacin jihar Borno dake iyaka da tafkin Chadi, inda ya ce wuri ne da aka san cewa akwai mayakan Boko Haram da dama.

Tokunbo Adesanya ya kara da cewa, jirage biyu ne suka kai harin, a ci gaba da luguden wuta kan gidajen da ake zargin muhalli ne ga mayakan Boko Haram da Rundunar sojin saman ta ke yi.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China