Ma'aikatar kula da albarkatu ta Sudan da hukumar binciken kimiyya da albarkatun kasa ta Masar sun ratabba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna don yin hadin gwiwa ta fuskar sanya ido kan girgizar kasa da hakar ma'adinai da mai.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, darakta janar na hukumar binciken ta Masar Mohammed Abu Fatma, ya ce yarjejeniyar da aka ratabbawa hannu a jiya Lahadi, za ta tanadi musayar bayanai tsakanin Sudan da Masar a matakin yanki, da ma duniya baki daya.
Da yake bayyana yarjejeniyar a matsayin mai muhimmanci, ya kuma yi bayanin cewa, ta samar da wata taswirar fasahar karkashin kasa, wadda ke da matukar muhimmanci da za ta iya bibiyar gudanar ruwan kogin Nile, musammam a lokacin ambaliya.
Yarjejeniyar ta kuma tanadi ba da horo ga jami'ai da bibiyar madatsu da ma'adanan ruwa da hakar ma'adinai da kuma ginin hanyoyi. (Fa'iza Mustapha)