in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahaukaciyar guguwar Irma ta sauka a yankin Florida na Amurka
2017-09-11 10:21:04 cri

A jiya Lahadi ne mahaukaciyar guguwar nan mai tafiyar kilomita 171 cikin sa'a guda mai suna Irma ta durfafi yankunan jihar Florida ta kasar Amurka.

Bayanai daga cibiyar nazarin mahaukaciyar guguwa ta kasa (NHC) na cewa, mahaukaciyar guguwar ta Irma ta haddasa ambaliyar ruwa a galabin tsakakiyar Miami, baya ga wasu kungiyoyin aikin gine-gine guda biyu da guguwar ta karya.

Hukumomin a jihar ta Florida sun kuma bayyana cewa, mahaukaciyar guguwar ta halaka mutane 27, Ko da yake ana fargabar adadin wadanda suka mutun na iya karuwa, yayin da ake tunanin mahaukaciyar guguwar za ta ratsa ta wasu cibiyoyin a yammacin Florida da ba su kimtsa mata ba.

Kafofin watsa labarai a yankin sun ba da rahoton cewa, mahaukaciyar guguwar ta haddasa katsewar layukan kama shirye-shiryen talabijin. Haka kuma mutane miliyan biyu a jihar ta Florida ba su da hasken wutar lantarki, cikinsu kuwa har da kashi daya bisa uku na yankin Miami-Dade dake kudu masu gabashin jihar.

Tun a ranar Asabar ne dai rundunar 'yan sandan jihar ta sanya dokar hana fita daga karfe 7 na yammacin ranar ta Asabar zuwa 7 na safiyar jiya Lahadi. Kana sashen jami'an 'yan kwana-kwana ba zai amsan kiran neman taimakon jama'a ba, a lokacin da iskar da mahaukaciyar guguwar take kadawa ya kai gudun kilomita 63 cikin sa'a guda.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China