in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cuba: An debe mutane 700,000 sakamakon matsowar guguwar Irma
2017-09-08 10:34:39 cri

Mahukunta kasar Cuba sun kwashe mutane kimanin 700,000 daga yankin gabar tekun kasar dake arewa maso gabashi, yayin da mahaukaciyar guguwa mai tattare da ruwan sama ke kara tikarar yankin yammacin Caribbean.

Hukumar kula da jin dadin jama'a ta kasar Cuba, ta ce guguwar mai lakabin Irma, ta yiwa yankin gabashi da tsakiyar Ciego de Avila tsinke, don haka ta bukaci gwamnatocin yankunan, da masu aikin ba da taimako, da su kasance cikin shirin tunkarar kalubalen da za ta haifar.

Tuni dai aka kwashe 'yan yawon shakatawa sama da 10,000 daga tsibirin dake daura da tekun yankin, yayin da kuma wasu ke tashi ta jiragen sama zuwa gida domin kaucewa abu da ka je ya zo.

Irma ta riga ta yi mummunar barna a yankunan Caribbean, inda ta hallaka a kalla mutane 15, tare da lalata gidaje da sauran ababen more rayuwa a tsibiran Antigua da Barbuda, da Puerto Rico, da St. Martin, da kuma arewacin gabar tekun janhuriyar Dominican.

An dai ce wannan ce mahaukaciyar guguwa mafi muni da ta taba aukawa wannan yanki na Atlantic. Kaza lika masana yanayi na ce, bayan arewacin Cuba, guguwar Irma za ta nausa zuwa jihar Florida ta kasar Amurka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China