in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministoci daga SADC sun sha alwashin sauya tsarin sadarwa a yankin
2017-09-08 09:30:57 cri

Ministocin hukumomin sadarwa na kasashe mambobin kungiyar SADC ta raya kudancin nahiyar Afirka, sun lashi takobin sauya tsarin sadarwa a kasashen su, ta yadda sashen zai zamo jigon samar da bayanai, da tattalin arziki mai dogaro kaco kan ga ilimi.

Kaza lika matakin zai taimaka, wajen hade sassan nahiyar waje guda, ya kuma agaza wajen daga matsayin sadarwa a daukacin sassan Afirka.

Hakan dai ya biyo bayan taro game da raya fannin fasahar sadarwa da ministocin yankin suka gudanar a birnin Durban na Afirka ta kudu. Taron ya kuma samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin tsara manufofi, da masu aiwatar da su, tare da jami'ai daga sashen raya fasahar sadarwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China