A jiya Laraba aka gudanar da taron kolin Sin da kasashen Larabawa kan kasuwanci da masana'antu a birnin Yinchuan da ke arewa maso yammacin kasar Sin, taron da ya kasance wani muhimmin bangare, na taron baje kolin kayayyakin Sin da kasashen Larabawa.
An dai fitar da sanarwar bayan taron, wadda ta yi nuni da cewa, Sin da kasashen Larabawa na iya taimakon juna matuka a fannin tattalin arziki, kuma suna iya inganta hadin gwiwarsu ta fannonin raya masana'antu, da samar da manyan ababen more rayuwa, da sadarwar zamani, da aikin gona da dai sauransu.(Lubabatu)