in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FIFA ta bada umarnin sake buga wata wasar neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya.
2017-09-07 12:44:08 cri
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bada umarnin sake buga wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta rukunin nahiyar Afrika da aka buga tsakanin Afrika ta kudu da Senegal, biyo bayan hukuncin da kotun musammam ta al'amuran da suka shafi wasanni ta yanke na haramtawa alkalin wasa Joseph Lamptey sake aiki tsawon rayuwarsa, saboda magudin wasa da ya yi.

A wasan da aka buga tsakanin bangarorin biyu a ranar 12 ga watan Nuwamban 2016, Joseph Lamptey ya ba Afrika ta kudu bugun da ga kai sai mai tsaron raga saboda taba kwallo da dan wasan tsakiya na Senegal Kalidou Koulibaly ya yi da hannu.
Wannan kwallo dai ita ce ta ba Afrika ta kudu nasarar lashe wasan, nasarar da ita ce ta farko da kasar ta samu tun fara buga wasannin rukuni.

Sai dai, hoton bidiyon wasan ya nuna a bayyane cewa, kwallon gwiwar Koulibaly kawai ta taba ba hannunsa ba sannan ta fadi kasa, don haka bugun daga kai sai mai tsaron raga da aka ba Afrika ta kudu bai dace ba. Kwamitin ladaftarwa da daukaka kara na FIFA ya kakabawa Joseph Lamptey haramcin shiga harkokin wasa na tsawon rayuwarsa saboda makarkashiya da ya yi, hukuncin da kotun ta tabbar.

A yanzu Senegal ce ta uku a rukunin da inda Cape Verde da Burkina Faso suka shige gabanta da maki guda. (Fa'iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China