Sakamakon wannan mataki, Amurka ta kammala shirin da ta yi, na sarrafa wadannan na'urori a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. To sai dai kuma wannan lamari ya gamu da adawa daga dandazon masu zanga zanga a Koriya ta kudun.
An ce dakarun rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma, sun tare gungun masu zanga zanga su kusan 8,000, kana da tsakar daren jiya, 'yan sandan suka tarwatsa wasu masu jerin gwano, da masu rajin nuna adawa da shirin su kusan 400, wadanda ke kewayen unguwannin Seongju da na birnin Gimcheon dake kan iyakar kasar.
Tarzomar nuna adawa da kafa na'urorin THAAD, ta sabbaba jikkatar a kalla mutane 30, wadanda aka garzaya da su asibiti mafi kusa, kamar dai yadda kafofin watsa labarun yankin suka tabbatar.
Tun cikin watan Yulin shekarar da ta gabata ne dai al'ummun yankunan da aka girke wadannan na'urori, da masu kin jinin shirin girke su, ke ta kunna kyandira a ko wane dare, a biranen Seoul na Koriya ta kudu da Washington na Amurka, a wani mataki na adawa da manufa.
Da ma dai ma'aikatar tsaron Koriya ta kudun ta tabbatar da shirin da ake yi, na girke ragowar na'urorin a ranar Alhamis. Ma'aikatar ta ce hakan ya biyo bayan gwaje gwajen makamai masu linzami ne da Koriya ta arewa ke faman yi ne a baya bayan nan. (Saminu)