in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar kungiyar nakasassun kasar Sin ta shiga zaben shugaban IPC
2017-09-07 12:08:38 cri

Yanzu haka ana gudanar da babban taron mambobin kwamitin wasannin Olympic ajin nakasassu na kasashen duniya wato IPC a birnin Abu Dhabi, fadar mulkin Hadaddiyar Daular Larabawa, taron da zai gudana tsakanin ranekun 5 da 9 ga watan da muke ciki.

Yayin taron za a gudanar da zaben sabon shugaban kwamitin. A jiya Laraba masu shiga takarar zaben guda hudu, sun gabatar da jawabansu daya bayan daya, inda jawabin da shugabar kungiyar nakasassun kasar Sin Zhang Haidi ta gabatar da Turanci kai tsaye cikin mintoci 15, ya fi jawo hankalin masu halartar taron.

Shugabar kungiyar nakasassun kasar Sin Zhang Haidi, ta gabatar da jawabinta ne kafin sauran uku, inda ta gabatar da jawabin da Turanci kai tsaye cikin mintoci 15, jawabin da ya fi jawo hankalin wakilai masu halartar taron, har sun yi tafi.

A cikin jawabin nata, Zhang Haidi ta yi kirayi ga wakilan da su nuna mata goyon baya, saboda idan suka nuna mata goyon baya, za su tabbatar da cewa, sun yi zaben da ya fi dacewa a nan gaba. Zhang Haidi ta ce, "Aminai, da 'yan uwanmu na babban iyalin kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasashen duniya, ina fatan za ku yi imani da nuna goyon baya gare ni, nan gaba za ku tabbatar da cewa, kun yi zabi mafi dacewa."

Cikin dogon lokaci, wato a cikin 'yan shekarun da suka gabata, Zhang Haidi ta kasance abin koyi ga al'ummun kasar Sin, musamman ma ga matasan kasar, bisa jarumtakar da take nunawa. An taba rubuta labaranta a cikin littafin da ake koyarwa ga daliban makarantar firamare na kasar Sin, ana kiranta da sunan yaya Haidi, dalilin da ya sa haka shi ne duk da cewa ita nakasasshiya ce, amma ba ta daina yin kokari ba, ko kan karatu ko kan aiki, har ta kasance abin koyi ga saura.

A cikin jawabinta, Zhang Haidi ta bayyana cewa, har kullum ta fi son taimaka wa saura, kuma tana gwaninta kan aikin jagoranci, ta ce, "Ina son taimakawa saura, ina da kirki, kuma ina himmantuwa kan aiki, kana ina matukar kaunar 'yan uwa a cikin babban iyalin nakasassu dake dukkanin fadin duniya. A kasar Sin akwai nakasassu sama da miliyan 85, na tattara fasahohi da dama yayin da nake samar da hidima gare su, hakan shi ma dalili ne dake samar da kwarewa a fagen aiki na ba da jagoranci, ina fatan za ku iya amincewa da anniyata, da karfina na ba da jagoranci a cikin kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya."

Zhang Haidi ta ci gaba da cewa, bisa matsayinta na nakasasshiya, ta fi sauran 'yan takarar fahimtar damuwa da fata na makasassu, kuma yanzu haka tana jagorancin aikin kula da makasassu a kasar Sin, a sa'i daya kuma tana jagorancin aikin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Sin, tawagoyin 'yan wasa nakasassu dake karkashin jagorancinta, sun zama zakaru a yayin gasar wasannin Olympic na nakasassu na duniya har sau hudu.

Zhang Haidi tana ganin cewa, ya kamata shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya fi gwaninta a fannonin son baki, da karfin ba da jagoranci, da kuma karfin samar da taimakon da ake bukata. A saboda haka ya dace a zabe ta don zama shugaban kwamitin. Ta ce, "Na yi alkawari cewa, zan yi iyakacin kokarina wajen taimakawa daukacin nakasassu, domin su samu waraka, da ilmi da aikin yi, kana zan goyi bayan su wajen gudanar da ayyukan al'adu, da kuma wasannin motsa jiki, duba da cewa wasannin motsa jiki za su sa kaimi gare su, yayin da suke kokarin samun waraka."

Wannan shi ne karo na farko da Basiniya ta shiga zaben shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana kara yin tasiri a fadin duniya, haka kuma ya alamta cewa, kasar Sin tana cike da imani wajen shiga sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na duniya, tana kuma son sauke nauyi dake wuyanta, tare da fatan kara taka rawa a fannin. An lura cewa, dalilin da ya sa hakan shi ne, kasancewar kasar Sin ta samu babban ci gaba a sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu. Zhang Haidi ta ce, (音响4)"A cikin 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta zuba jarin da yawansa ya kai dalar Amurka sama da biliyan daya, kan sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu, an kuma kafa cibiyoyin horas da 'yan wasa nakasassu a matsayi na kasa har 32. Yanzu haka kuma nakasassu kusan miliyan 8 suna motsa jiki yau da kullum, kana tawagogin 'yan wasa nakasassu na kasar Sin, su ma sun samu babban sakamako, a yayin gasar wasannin Olympic ajin nakasassu na duniya."

Jawabin da Zhang Haidi ta gabatar ya samu karbuwa sosai daga wakilai mahalartan taron.

Ban da Zhang Haidi, sauran 'yan takarar a zaben su uku, sun hada da Patrick Jarvis na kasar Canada, da Andrew Parsons na kasar Brazil, da John Peterssen na kasar Denmark, kuma za a sanar da sakamakon zaben a gobe Jumma'a ranar 8 ga wata. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China