in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai sauran rina a kaba game da yanayin tattalin arzikin Najeriya
2017-09-06 11:08:40 cri

Mai ba da shawara na musamman ga shugaban Najeriya a fannin tattalin arziki Adeyemi Dipeolu, ya ce duk da cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arziki da ta sha fama da shi, akwai sauran kalubale, muddin ba a kaucewa wasu manufofi, da ka iya kara dagula al'amura ba, baya ga wasu al'amura na kasa da kasa da ka iya shafar tattalin arzikin Najeriyar.

Mr. Dipeolu ya yi wannan tsokaci ne, biyowa bayan alkaluman da hukumar kididdiga ta Najeriyar NBS ta fitar, wadanda suka bayyana cewa kasar, ta samu fita daga komadar tattalin arziki cikin watanni 3 na biyu na wannan shekara ta bana.

Cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar, jami'in ya ce, yanzu haka lokaci ya yi da gwamnati za ta matsa kaimi, wajen tabbatar da nasarar manufofin nan na ERGP, wadanda aka tsara musamman don ganin dorewar farfadowar tattalin arzikin kasar.

Hakan a cewar sa, zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriyar, ya fadada damammakin samun kudin shiga, da kara yawan guraben ayyukan yi, tare da bunkasa yanayin gudanar sana'o'i da cinikayya.

Dipeolu ya ce, matsalar karancin guraben ayyukan yi tana da tsanani, kuma sai an samar da wannan dama ne, sauran sassa na hada hadar cinikayya, da guraben ayyukan yi za su fadada, matakin da kuma zai haifar da kyakkyawan yanayi, na bunkasar tattalin arziki da cinikayya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China