in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaran Mozambick na fatan zurfafa hadin gwiwa da CRI
2017-09-05 13:08:38 cri

A safiyar jiya Litinin, daraktar ofishin watsa labarai na kasar Mozambick madam Emilia Jubileu Moiane, da sauran wakilan ofishin shida sun ziyarci gidan rediyon kasar Sin wato CRI, inda suka tattaunawa da mataimakin babban editan CRI Ren Qian.

Yayin tattaunawarsu, Mr. Ren Qian ya bayyana cewa, a shekarar 2013, wasan kwaikwayon kasar Sin "Doudou da da surukanta" ya samu karbuwa daga masu kallon telebijin a kasar ta Mozambick, kuma a nan gaba ya dace a ci gaba da yin kokari wajen samar da makamantan sa, duba da cewa haka zai taka rawa wajen yada al'adun kasar Sin a kasar ta Mozambick dake nahiyar Afirka.

A nata bangare, daraktar ofishin watsa labarai ta kasar Mozambick madam Emilia Jubileu Moiane ta yi nuni da cewa, kafofin watsa labarai na kasar Sin sun samu ci gaba cikin sauri, kuma CRI da sauran manyan kafofin watsa labarai na kasar Sin, sun kasance abun koyi ga kafofin watsa labarai na Mozambick. Don haka tana sa ran cewa, za a kara karfafa aikin cudanya tsakanin ma'aikatan kafofin watsa labarai na sassan biyu, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwa da fahimtar juna, da kuma zumuncin dake tsakanin kasashen biyu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China