in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin Xi a taron masana'antu da kasuwanci na BRICS zai sa kaimi ga ci gaban kungiyar a shekaru 10 masu zuwa
2017-09-04 10:59:27 cri

Da yammacin jiya Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bikin bude taron masana'antu da kasuwanci na kasashen wakilan kungiyar BIRCS, wanda aka gudanar a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudancin kasar Sin, inda kuma ya gabatar da jawabi.

Kwararrun a fannin sun bayyana cewa, jawabin na shugaba Xi zai sa kaimi ga ci gaban kungiyar BRICS a cikin shekaru goma masu zuwa, kuma ko shakka babu, tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS zai kara bunkasa yadda ya kamata.

Daraktan cibiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS ta jami'ar horas da malaman makaranta ta birnin Beijing Wang Lei yana ganin cewa, tun daga shekarar 2010, taron masana'antu da kasuwancin kasashen BRICS, ya riga ya kasance wani muhimmin dandali na cudanya ga 'yan kasuwa na kasashen, haka kuma tarukan da aka gudanar sun taka muhimmiyar rawa, wajen ci gaban tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen kungiyar, tare kuma da samar da taimako ga kamfanonin kasashe daban daban, domin su shiga tsarin kai tsaye. Wang Lei ya ce,"Taron masana'antui da kasuwancin kasashen BRICS yana da tsari mai inganci, kuma yana samun kyautatuwa karkashin kokarin da ake yi, misali kamfanonin kasashen BRICS suna gudanar da hadin gwiwar tsakaninsu kai tsaye, kuma shugabannin kasashen suna iya lura da wasu matsalolin da kamfanonin suke fuskanta, haka ne ya sa shugaba Xi Jinping ya bayyana cikin jawabinsa cewa, kamata ya yi kasashen BRICS su kara mai da hankali ga hadin gwiwar dake tsakaninsu, ba wai gudanar da shawarwari kadai ba."

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana babban taken hadin gwiwar kasashen BRICS daga fannoni uku kamar haka: na farko, nuna sahihanci ga juna bisa matsayin daidai wa daida, na biyu, kara gudanar da hadin gwiwa domin samun ci gaba tare, na uku, kara mai da hankali kan babbar moriyar daukacin kasashe a fadin duniya domin amfanawa al'ummomin kasashen duniya baki daya.

Manazarci kan huldar kasa da kasa ta zamanin yanzu ta kasar Sin Chen Fengying tana ganin cewa, babban taken hadin gwiwar kungiyar BRICS da shugaba Xi ya bayyana, ba ma kawai ya nuna mana cewa shi ne dalilin da ya sa ake samun babban sakamako yayin da ake gudanar da hadin gwiwa mai zurfi tsakanin kasashen BRICS ba, har ma hakan na nufin za a aiwatar a nan gaba, tana mai cewa, "Da farko, shugaba Xi ya bayyana cewa, abu mafi muhimmanci shi ne nuna sahihanci wajen daukar matsayi na daidai wa daida, ina ganin cewa, wannan shi ne tushen gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS. Na biyu, ya kamata a mai da hankali kan hakikanin yanayin da ake ciki yayin da ake gudanar da hadin gwiwa, wato dole ne a tabbatar da hadin gwiwa maimakon yin shawarwari kadai. Banda haka, shugaba Xi na ganin cewa bai kamata ba, a mai da hankali kan moriyar kai kadai ba, maimakon haka ya dace a maida hankali kan babbar moriyar al'ummomin kasashen duniya baki daya, musamman ma al'ummun kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki, da kuma kasashe masu tasowa."

Kana Chen Fengying ta bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana ganin tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS bai gudana yadda ya kamata ba. Game da hakan, shugaba Xi ya bayyana cewa, duk da cewa, ana fuskantar kalubale, amma dole ne a yi kokari matuka wajen dakile matasaloli, da kuma ganin ta yaya za a tattauna wadannan batutuwa yayin taron da ake gudanarwa.

Kazalika, shugaba Xi ya bayyana cikin jawabin na sa cewa, kasar Sin za ta kara zurfafa kwaskwarima daga duk fannoni a fadin kasar, ta yadda za ta samu ci gaba tare da sauran kasashen BRICS. Daraktan cibiyar hadin gwiwar tsakanin kasashen BRICS na jami'ar horas da malaman makaranta ta birnin Beijing Wang Lei na ganin cewa, matsalolin da ake fuskanta ba za su kawo illa ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS ba, Wang Lei ya ce, "Daga jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ana iya lura da cewa, ana cike da imani kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS, dalilin da ya sa haka kuwa shi ne, ganin yadda ake gudanar da hadin gwiwa lami lafiya, kuma ana ci gaba da kokari. Game da matsalolin da ake fuskanta kuwa, ana iya warware su sannu a hankali ta hanyar yin kwaskwarima."

A karshe dai, shugaba Xi ya nuna fatansa kan ci gaban kasashen BRICS a shekaru goma masu zuwa a fannoni hudu. Wato na farko a fannin kara zurfafa hadin gwiwar tsakaninsu domin bunkasa tattalin arzikin kasashe mambobi. Na biyu kuwa shi ne sauke nauyin dake wuyan kasashen kungiyar wajen kiyaye zaman lafiya a fadin duniya. Sai na uku, kara kyautata tsarin tattalin arzikin duniya. Na hudu kuwa shi ne kara habaka tasirin kasashen BRICS a fadin duniya, domin habaka huldar abokantaka dake tsakaninsu da sauran kasashe. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China