Cikin wani sako na Tweeter, Mr. Trump ya ce kalamai da ayyukan mahukuntan Koriya ta Arewa na da matukar hadari, don haka ya ce zai gana da shugaban ma'aikata na fadar White House John Kelly, da sakataren tsaro James Mattis, tare da wasu kusoshin rundunar sojin kasarsa domin tattauna halin da ake ciki.
A wani ci gaban kuma, wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bayyana rashin amincewar kasar da matakin na Koriya ta Arewa, tana mai Allah wadai da gwajin wannan makami na nukiliya.
Sanarwar ta ce Koriya ta Arewa ta yi kunnen uwar shegu da kiraye kirayen da kasashen duniya ke mata, na kauracewa gwajin makaman nukiliya, don haka ko alama, gwamnatin Sin ba ta goyi kasar game da wannan batu. (Saminu Hassan)