Kuma ana sa ran ba da sabuwar shawara dangane da hadin gwiwar kasashe masu tasowa a wajen taron.
Ana ganin cewa, taron shugabanni ta wannan karon, zai habaka hadin gwiwar kasashen BRICS, inda kuma ake son ci gaba da tattaunawa kan shawarar "BRICS+" da kasar Sin ta fitar.
Ana iya samun bayani kan taron shugabannin kasashen BRICS karo na 9 a shafin intanet na musammam da aka samar don taron, inda kasar Sin ta ba da shawarar kyautata tsarin hadin gwiwar kasashen, ta fuskar habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu, har ma da sauran kasashe abokan hulda, ta yadda za a samar da wani tsari da kasar Sin ta kira da "BRICS+".
Bugu da kari, a halin yanzu, yin shawarwari da hadin gwiwa da kasashe masu tasowa domin neman ci gaba tare ya kasance wata kyakyyawar al'ada ta taron shugabannin kasashen BRICS. (Maryam)