in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na son kara inganta hadin gwiwar kasashen BRICS tare da takwarorinta
2017-09-01 21:27:51 cri
A gun taron manema labarai da aka shirya a yau Jumma'a a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasancewarta kasa da ke jan akalar shugabancin kasashen BRICS a wannan shekara, Sin na son kara inganta hadin gwiwar kasashen BRICS, tare da takwarorinta da ke cikin kungiyar, don aza harsashi mai inganci na hadin gwiwar kasashen nan da shekaru 10 masu zuwa.

Kakakin ta ce, a cikin shekaru 10 da suka wuce tun bayan kafuwar kungiyar, kasashen BRICS sun yi ta kara taka muhimmiyar rawa, ta fannin bunkasa tattalin arzikin duniya, da gyaran tsarin duniya, da kuma kiyaye zaman lafiya a duniya.

Kakakin ta kuma kara da cewa, har kullum kasashen BRICS na dukufa a fannin hadin gwiwa tare da sauran kasashe masu tasowa.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China