in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitin tafi da gidanka na sojojin ruwan kasar Sin "Peace Ark" na ba da jinya kyauta a Afirka
2017-08-31 13:21:24 cri

Jirgin ruwa dake ba da hidimar jinya mai suna "Peace Ark" na sojojin ruwan kasar Sin ya ziyarci kasar Djibouti daga ranar 23 zuwa ranar 31 ga wata, don bai wa jama'ar kasar jinya kyauta, hidimar da ta samu karbuwa sosai, ya zuwa yanzu dai yawan mutanen da suka samu jinya ya kai dubu daya. Wannan ne karo na shida da jirgin ruwa da ke da asibitin tafi da gidanka mai suna "Peace Ark" ya gudanar da irin wannan aiki. Guan Bolin, jagoran aikin na shekarar bana ya bayyana cewar, an gudanar da aikin ne don ba da taimakon jin kai, da yada manufofin kasar Sin na neman samun zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa don samun moriyar juna, tare kuma da nuna yadda kasar Sin ke daukar nauyi dake wuyanta.

A ranar 26 ga watan Yuli ne, jirgin ruwan dake ba da tallafin kiwon lafiya na sojojin ruwan kasar Sin wato "Peace Ark" ya tashi daga wata tashar jiragen ruwan soja da ke tsibirin Zhoushan na kasar don kaddamar da aikinsu na ba da jinya kyauta na bana. Daga baya ne, zai ziyarci kasashen Djibouti, Saliyo, Gabon, Jamhuriyar Kongo, Angola, Mozambique, Tanzania, kana da Timo ta gabas da ke nahiyar Asiya, aikin da zai kwashe kwanaki 155 ana yinsa. Wannan ne karo na shida da jirgin ruwan ya kaddamar da irin wannan aikin.

Yayin da yake bayani game da ma'anar gudanar da aikin, Janar Guan Bolin, jagoran aikin ya bayyana cewa,

"Aikin ba da jinya kyauta na shekarar 2017 wani muhimmin aikin soja ne ta fuskar diplomasiyya na bana, wanda ya samu izni daga hukumar kula da harkokin soja na kwamitin tsakiya na JKS. Aikin wani bangare ne na shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasarmu ta gabatar, kana wani aikin gwaji ne da sojojin ruwan kasarmu suka yi na zuwa wurare masu nisa don aikin kiwon lafiya, a kokorin inganta aikin samar da jituwa."

Wannan shi ne karo na hudu da Janar Guan Bolin ya shiga aikin ba da jinya kyauta, kuma karo na biyu da ya ke jagorantar aikin, yana ganin cewa,

"Jirgin ruwan da ke aikin ba da hidimar jinyar wato 'Peace Ark' ya gudanar da aikin ne don ba da taimakon jin kai, da yada manufofin kasar Sin na neman samun zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa don samun moriyar juna, tare kuma da nuna wa duniya wata babbar kasa da ke iya daukar nauyi dake wuyanta, da wata rundunar sojojin ruwa da ta kara bude kofa, da kara nuna imani."

Rahotanni na cewa, a yayin aikin na bana, jirgin da ke ba da hidimar jinyar "Peace Ark" yana dauke da wani jirgin sama mai saukar ungulu, da kuma kwararrun likitoci 115 daga jami'ar koyar da ilmin likitanci ta sojojin ruwa, da babban asibitin sojojin ruwa da sauran hukumomin kiwon lafiya 19 na kasar Sin. A cikinsu, akwai wani likita mai suna Sun Tao, wanda ya shiga aikin ba da jinyar tun daga shekarar 2009, kawo yanzu ya shiga aikin har sau shida.

Sun Tao ya bayyana cewa, jirgin ruwa na "Peace Ark" ya gudanar da aikin ba da jinya kyauta ne don yada manufofin kasar Sin na neman samun bunkasuwa cikin lumana, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, lamarin da ya sa aka kara fahimtar likitocin kasar Sin ta fuskar kaunar duniya. Jirgin dake ba da hidimar jinyar wani babban dandali ne na kiwon lafiya, inda ake magance wasu cututtuka masu sarkakiya. Domin kawo sauki ga jama'ar kasashe daban daban masu tasowa a fannin ganin likita, za kuma a tura kungiyoyin jinya daban daban na jirgin ruwan don zuwa makarantu, gidajen marayu, da gidajen kula da tsoffi don samar da aikin jinya. Idan an gamu da mutanen da suka kamu da cututtuka masu tsanani, za a kai su jirgin ruwan don ba su jinya da yi musu tiyata idan akwai bukatar hakan.

A ganin Sun Tao, jirgin ruwan na "Peace Ark" ya fara ziyarar kasashen Afirka tare da samar da jinya kyauta ta jin kai a bana, lamarin da ya inganta hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya. Ya kara da cewa,

"Tura kungiyoyin likitoci zuwa kasashen Afirka wani muhimmin bangare ne na samar da taimakon jinya ga ketare da kasar Sin ke yi. A ganina, ziyarar Afirka da jirgin ruwa na 'Peace Ark' ke yi, ta kara haske ga aikin hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China